Game da mu | Alaka da mu |
Barka da zuwa sayet din Imam Mahadi (A.S) info@imamalmahdi.com

Takaitaccen Tarihin Rayuwar Malam Ibrahim Yaqub Zakzaky

Rana da wajen da aka haifi Sheikh:
An haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953[15 ga Sha'aban 1372 AH] a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'. Sheikh Ibrahim Zakzaky shine dan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan Tajuddin dan Hussain. Shi Hussain wani bawan Allah ne da ya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodio[RA] ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a lokacin da Shehu Usman dan Fodio[RA] ya nada Mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin iayalen su kuma suka zama yan uwan juna ta wannan tun a farkon karni na 19. Mahaifin Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rasu ne tun shekara ta 1972, sai dai mahaifiyar sa har yanzun tana nan raye, Sheikh shine na biyar a wajen mahaifin su. Karatun sa:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake Zaria. Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon larabci ta Kano watau School for Arabic Studies[SAS] wadda aka gina tun 1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. Kusan baki dayan alkalin alkalan jihohin Arewa daga wannan makaranta suka sami horon su. Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin fadada ilmin sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba kamar sanin gwamnati [Government] da ilmin tattalin arziki[Economics] inda yayi jarabawar GCE a kansu. Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta gaba[Advanced level GCE] akan wadannan maddojin:Government, Economics,Hausa,da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979 inda ya fara karatun digirin farko [B. Sc] akan sanin tattalin arziki [Economics]. Sheikh yayi musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a cikin makaranta da kuma? matsayin kasa baki daya inda a shekara ta 1978 ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga Shari'ah a baki dayan kasar. Sheikh Zakzaky bisa sha'awar da yake da ita na fadada karatun sa ya ci gaba da zuwa wajen malamai da suka hada da Malam Sani Abdulkadir, Malam Isa na Madaka, Malam Sani Na'ibi da kuma Malam Ibarhim Kakaki dukkanin su a birnin Zaria. Haka nan kuma a Kano Sheikh yayi karatu wajen Shawish Abdallah na Sagagi da Malam Nuhu limamin Yola. Tafiye-Tafiyen sa:
Sheikh Zakzaky yayi tafiya zuwa kasashe kamar su Britaniya, Saudi Arabia, Iran, Lebanon, Afrika ta kudu, Amurka, da Rasha. Dukkanin wadannan tafiye-tafiye yayi sune ta hanyar gayyata don dalilai na addini ko halartan tarurrukan karawa juna ilmi. Mata da yara:
Sheikh yana da mace daya da kuma yaya tara. • http://www.almawood.net
  http://www.hazratmahdi.com
  http://www.baqiyatullah.com
  http://www.majaalis.com
  http://www.baqiatollah.org
  http://www.al-mahdi.org
  http://www.imammahdi.com
  http://www.yamahdi.com
  http://www.imammahdi-s.com
  http://www.14masom.com
  http://www.jamkaran.info
  http://www.alqaem.net
  http://www.mahdieh.org
  http://www.hazratesaheb.com
  http://www.montazar.net
  http://www.ejlasmahdi.com
  http://www.monjee.org
  http://www.hazratmahdi.com
  http://www.mouood.com
  http://www.imammehdi.org

  Tun daga lokcin fakuwa da boyuwar imam Mahadi (A.S) wato; lokacin sheikh Mufid har zuwa wannan lokaci namu imam Mahadi (A.S) ya yi ludufi na musamman mai yawa ga manyan malamai masana masu aiki da iliminsu, har suka samu damar haduwa da imam Mahadi (A.S) da saduwa da shi, kuma wannan ya taimaka musu matuka wajan shiryar da mutane da rayar da zukatansu.

  Yin wata daura ta koyarwa da kuma sanin imam Mahadi (A.S) musamman ga dalibai wadanda suka zo daga kasashe 22 na duniya game da imam Mahadi (A.S) a cikin kur'ani tun daga gabatarwa har zuwa manyan kosa-kosai kowanne wata 6 ne ta hanyar Ayatul-Lahi sayydi Mahamud Baharul Ulum a garin Kum.

  Bayanai game da tafiyar Ayatul-Lahi sayydi Mahamud Baharul Ulum Mirdamadi zuwa kasashe daban-daban musamman turai da kuma ziyartar masallatai, da coci-coci, da wuraren bauta, da husainiyyoyi, da cibiyoyi, da kungiyoyi, da jami'o'I, da wuraren tarihi, da zama da limaman masallatai, da pada-pada, da malaman yahudawa, da wakilan cibiyoyi, da shugabannin mazhabobi, da mutane daban-daban, da kuma yin laccoci a wurare mabanbanta da kuma kwadaitarwa game da karbar addinin musulunci da mazhabar shi'anci da bishara da bayyanar imam mahadi (A.S) a karshen zamani.

  Suna : Imel :
  عربي فارسي English French اردو Italiano
  Turkish Русский Azəri Hausa  Indonesia Thai Bangla
  Copyright © 2000 - 2008 - Dukkan hakkoki sun damfaru da cibiyar bincike ta Waliyyul Asr imam Mahadi (A.S) ne Sarkar gizo-gizo ta duniya ta bayanai game da imam Mahadi (A.S).
  Yanayin addini
  Masu tunani da imam Mahadi
  Yanayin tattalin arziki
  Komitin ranakun rahama na mahadiyyanci
  Adalcin Allah da samuwar imam Mahadi
  Muhimmancin imam Mahadi
  Jagorancin imam Mahadi
  Amfanin boyayyen imami
  Hikimar imani da mai tseratarwa
  Gamemman tunani game da imam Mahadi
  Menene ya hau kanmu
  Alamomin bayyanar imam Mahadi
  Rijista
  Fasa Rijista