Home Page | About US | Contact Us |
 

Raja’a: Komowa Duniya

Abin da Mazhabar Ja’afariyya Imamiyya ta tafi a kansa da riko da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) Shi ne cewa; Allah (S.W.T) zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma saka wa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).

Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna, sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashin kiyama, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuma azaba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Kur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu, to mun yi furuci da zunubanmu, shin akwai wata hanyar fita”. Surar Mumin: 11.

Na’am Kur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, kuma mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa, ma’anarta ita ce komowar hukuma da umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S), da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko rayar da matattu.

Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya, kuma aibi gare shi da yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da aibata su da shi.

Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsawon zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai janyo wannan ba, domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa, kuma ita tamkar mu’ujizar rayar da matattu ce da ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma, domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. Surar Yasin: 79-87.

Amma wanda ya soki Raja’a kuwa bisa dalilin cewa tana daga cikin “Tanasuhi[1]”, wannan saboda bai fahimci bambanci tsakanin “Tanasuhi” da tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba ne, ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da matattu da jikinsu ne, domin ma’anar Tanasuhi ita ce: Ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba. Wannan kuwa ba ita ce ma’anar tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba, ma’anarta ita ce; komo da ainihin jikin da siffofinsa na kashin kansa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa da “Raja’a” “Tanasuhi” ce, to rayar da matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) ma ya zama “Tanasuhi” ne, haka ma tayar da matattu da komo da ainihin jikkunansu ya zama “Tanasuhi’’ ke nan.

Saboda haka babu abin da ya rage sai tattaunawa game da “Raja’a” ta fuska biyu.

(1) Na farko: Cewar ita mustahiliya ce.

(2)Na biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.

(1)A bisa kaddarawar cewa tattaunawar guda biyu daidai ne, to yin imani da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu gaba da Shi’a suka mayar da ita, kuma da yawa daga cikin abubuwan da suke mustahilai ne wasu bangarorin musulmi suka yi imani da su, ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalai masu dama a kan hakan, kamar imani da yiwuwar rafkanwa ga Annabi (S.A.W) ko kuma aikata sabo, da kuma imani da rashin farko ga Kur’ani, da kuma batun narkon azaba, da kuma imani da cewa Annabi bai yi wasiyya da halifa a bayansa ba.

Kuma wadannan munakashoshi biyu ba su da wani asasi na inagnci, amma batun cewa raja’a mustahili ce mun riga mun kawo cewa ita nau’i ce na tayar da matattu da jikkunansu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili a kan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili a kan cewa dole ta zama abin mamaki, sai dai kawai mu ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya, ba mu san kuma sabubbanta da abubuwan da suke hana ta ba da zasu sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce masa: “Wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. (Yasin: 78-79)

Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali a kai na tabbatar da shi ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin samuwar dalili, to a nan ya zama dole a kanmu mu koma wa nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Kur’ani kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta rayar da matattu: “Kuma Ina warkar da Wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49.

Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai rayar da wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi Shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259.

Da kuma ayar da ta gabata da take cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba zata yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba, duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba, kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba.

(2) Tattaunawa ta biyu:- Ita ce da’awar cewa hadisai game da Raja’a kagaggu ne, ba ta da asasi, domin Raja’a tana daga cikin al’amuran da suke na larura da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) na hadisai mutawatirai.

Bayan wannan, ashe ba ka yi mamakin shahararren marubucin nan mai da’awar sani Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, da yake cewa; “Yahudanci ya bayyana a cikin Shi’anci ta hanyar imani da Raja’a”. Don haka ni nake cewa masa: “Ashe kenan Yahudanci ma ya bayyana a Kur’ani saboda batun Raja’a”. Kamar yadda ya gabata game da ayoyin Kur’ani mai girma da suka ambaci Raja’a.

Kuma zamu kara masa da cewa: A hakika babu makawa wasu akidun Yahudanci da Kirintanci su bayyana a cikin da dama daga akidu da hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi mai girma (S.A.W) ya zo yana mai gaskata Shari’o’i da suka gabata, duk da yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. Don haka bayyanar Yahudanci da Kiristanci a wasu abubuwan da musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin musulunci, wannan idan har an kaddara cewa Raja’a tana daga akidojin Yahudawa kenan kamar yadda wannan marubucin yake da’awa.

Ko yaya dai, Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita, kuma aukuwarta ba mustahili ba ne.


[1] - Tanasuhi shi ne ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba.